1 Peter 5

Zuwa ga Dattawa da kuma Samari

1Zuwa ga dattawan da suke cikinku, ina roƙo a matsayin ɗanʼuwanku dattijo, mashaidin shan wahalar Kiristi wanda kuma shi ma zai sami rabo cikin ɗaukakar da za a bayyana: 2Ku zama makiyayan garken Allah da yake a ƙarƙashin kulawarku, kuna hidima kamar masu kula-ba kan dole ba, sai dai da yardar rai, yadda Allah yake so ku zama; ban da kwaɗayin kuɗi, sai dai marmarin yin hidima; 3ban da nuna iko a kan waɗanda aka danƙa muku amana, sai dai ku zama gurbi ga garken. 4Saʼad da kuwa Babban Makiyayin ya bayyana, za ku karɓi rawanin ɗaukaka marar koɗewa.

5Samari, ku ma, ku yi biyayya ga waɗanda suka girme ku. Dukanku, ku yafa sauƙinkai ga juna, domin,

“Allah yana gāba da mai girmankai,
amma yakan yi alheri ga mai sauƙinkai.”
K Mag 3.34

6Saboda haka, ku ƙasƙantar da kanku a ƙarƙashin hannun Allah mai ƙarfi, don yǎ ɗaukaka ku a lokacin da ya ga dama. 7Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku.

8Ku zama masu kamunkai, ku kuma zauna a faɗake. Abokin gābanku, Iblis yana kewayewa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai cinye. 9Ku yi tsayayya da shi, kuna tsayawa daram cikin bangaskiya, domin kun san cewa ʼyanʼuwanku koʼina a duniya suna shan irin wahalolin nan.

10Allah mai dukan alheri, wanda ya kira ku ga madawwamiyar ɗaukaka cikin Kiristi, bayan kun sha wahala na ɗan lokaci, shi da kansa zai raya ku, yǎ kuma sa ku yi ƙarfi, ku kahu, ku kuma tsaya daram. 11Gare shi bari iko yǎ tabbata har abada abadin. Amin.

Gaisuwar Ƙarshe

12Da taimakon Sila, wanda na ɗauka a matsayin ɗanʼuwa mai aminci, na rubuta muku a taƙaice, ina ƙarfafa ku ina kuma shaida muku cewa wannan shi ne alherin Allah na gaske. Ku tsaya daram a cikinsa.

13Ita wadda take a Babilon, zaɓaɓɓiya tare da ku, tana gaishe ku, haka ma ɗana Markus. 14Ku gai da juna da sumbar ƙauna. Salama gare ku duka da kuke cikin Kiristi.

Copyright information for HauSRK